Connect with us

News

Filayen Kuyan Ta Inna: Gwamnatin Tarayya Na Ci Gaba Da Aiki Duk Da Umarnin Kotu

Published

on

IMG 20250621 WA0012

Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aikin shimfiɗa layin dogo a filayen Kuyan Ta Inna da ke Kano, duk da hukuncin kotu da ya hana ci gaba da aikin.

Fiye da masu filaye 75 ne suka maka Ma’aikatar Sufuri da kamfanin da ke aikin da kuma hukumomin tsaro a kotu, bayan da suka ce ana ƙoƙarin kwace musu filayen ba tare da biyan diyya ko bin doka ba.

Advertisement

Mutane 7 Sun Gamu Da Ajalinsu A Harin Da Matasa Suka Kai Kan Motar Bas A Filato

Rahotanni daga yankin sun ce a ranar 19 da 20 ga Yuni, an ga ma’aikatan kwangilar aikin a filayen suna ƙoƙarin share ƙasa domin ci gaba da aiki, lamarin da ya saba da umarnin kotu.

Wata majiya ta shaida wa Jaridar NIGERIAN TRACKER cewa, “Mun nuna musu takardar hukuncin kotu, amma sun ce ba su sani ba. Duk da haka sun ci gaba da kokarin aiki.”

Advertisement

A cewar NIGERIA TRACKER, yawancin waɗanda ke da filayen marasa galihu ne da marayu, kuma filayen na cikin wuraren da gwamnati ta amince da su.

Yanzu haka dai ana jiran matakin da kotu ko gwamnati za su ɗauka kan zargin take doka da rashin kulawa da hakkokin ‘yan ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending