Connect with us

News

JAMB Ta Ƙayyade Mafi Ƙanƙantar Makin Shiga Jami’a Da Kwaleji

Published

on

jamb exam1 (1)

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya, wato JAMB, ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin da ɗalibi zai samu domin samun gurbin karatu a jami’o’in ƙasar nan a shekarar karatu ta 2025.

Wannan matsaya ta fito ne daga wani taro na musamman da hukumar ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, inda aka tattauna tsarin karɓar sabbin ɗalibai a manyan makarantu na gaba da sakandire.

Advertisement

ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni

A cewar JAMB Ɗaliban da suka nemi shiga jami’o’i dole ne su samu aƙalla maki 150,kwalejojin koyon aikin jinya, an sanya maki 140, Sai kuma maki 100 ga waɗanda ke neman shiga kwalejojin ilimi da aikin noma.

Wannan ƙayyadadden mataki ya biyo bayan faduwar da aka samu a sakamakon jarabawar JAMB ta bana, inda rahotanni suka nuna cewa ɗimbin ɗalibai sun kasa kai har zuwa matsakaicin maki.

Advertisement

A bangaren wasu iyaye da ƙwararru a fannin ilimi, sun bayyana damuwa kan yadda ƙananan maki za su iya shafar ingancin ɗalibai da ake karɓa a jami’o’i da sauran manyan makarantu.

Sai dai JAMB ta ce ta dauki matakin ne domin bai wa ɗalibai dama, musamman waɗanda suka yi jarrabawar bana a ƙarƙashin matsin lamba da ƙalubale da dama.

Advertisement

Hukumar ta kuma ce za ta ci gaba da sa ido kan tsarin tantance ɗalibai da tabbatar da cewa an karɓi waɗanda suka cancanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending