News
Attajiran Afrika 4 ne ke riƙe da fiye da rabin arziƙin nahiyar —Oxfam
Wani rahoto da Oxfam ta fitar a yau Alhamis ya nuna yadda Attajiran Afrika 4 kaɗai ke riƙe da arziƙin da ya ɗara na rabin al’ummar nahiyar baki ɗaya.
Nahiyar mai yawan jama’a fiye da miliyan 750 da ke fama da tarin matsaloli masu alaƙa da talauci baya ga rashin daidaito, a cewar ƙungiyar mai rajin yaƙi da talauci halin da ake ciki na barazana ga ɗorewar Demokraɗiyya.
An Kama ‘Yan Najeriya Kan Zargin Aikata Zamba Ta Intanet A Pakistan
Duk da cewa rahoton na Oxfam ya bayyana sunan Attajiri Aliko Dangote ne kaɗai a sahun attajiran 4 da ke riƙe da fiye da rabin arziƙin nahiyar ta Afrika, amma mujallar Forbes ta bayyana sunayen Johann Rupert da Nicky Oppenheimer ƴan Afrika da kudu da kuma Nassef Sawiris na Masar a matsayin cikon ukun mafiya arziƙi a nahiyar.
A cewar Oxfam attajiran na Afrika sun samu ƙarin kashi 56 cikin ɗari na arziƙinsu a shekaru 5 da suka gabata, dai dai lokacin da gamagarin al’ummar nahiyar ke ci gaba talaucewa tare da fuskantar rayuwa mai cike da uƙuba.
Rahoton na Oxfam ya ce fiye da rabi daga cikin ƙasashe 50 mafiya fuskantar matsalolin rashin daidaito da talauci na a nahiyar ta Afrika.
Oxfam ta ce galibi dokoki da manufofin gwamnatocin nahiyar ta Afrika na tsaurarawa talakawa ne tare da buɗe hanyar azircewa ga mawadata.
Rahoton ya ci gaba da cewa akwai matuƙar banbanci ga tsarin biyan haraji tsakanin Matalauta da Mawadata a ƙasashen Afrika ta yadda ake tatse Talakawa ake kuma sauƙaƙawa masu kuɗi.
