News
Kotu ta yi watsi da ƙarar da Abba Hikima ya shigar a madadin mabaratan Abuja
Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da ƙarar da wani lauya, Barista Abba Hikima, ya shigar a madadin wasu marasa galihu da suka haɗa da masu bara, ‘yan talla da masu jari bola, inda suka nemi kotu ta tilasta gwamnatin tarayya ta biya su diyyar Naira miliyan 500 bisa zargin take haƙƙinsu.
A cikin ƙarar da aka shigar, an zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da kuma Sufeto Janar na ’Yan sanda da cin zarafin waɗannan mutane ta hanyar kama su ba bisa ƙa’ida ba, tsare su ba tare da tuhuma ba, da kuma karɓar kuɗi daga hannunsu da ƙarfi da yaji, matakin da suka ce ya sabawa dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da na duniya.
Lauyoyin Gwamnatin Kano Zasu Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Sai dai, a zaman kotun da aka yi ranar Juma’a, 11 ga Yuli, 2025, Mai Shari’a James Omotosho ya yanke hukunci da ke bayyana cewa ƙarar ba ta da wata tushe balle makama, tare da jaddada cewa kotu ba ta ga wani dalili na hukunta wadanda ake ƙara ba.
Babu Gamsasshiyar Hujja – Inji Kotu
A cewar Mai Shari’a Omotosho, takardun da mai ƙara ya gabatar a gaban kotu ba su nuna wani sahihin hujja da ke tabbatar da cin zarafin da ake zargi ba. Ya ce mafi yawan hujjojin sun dogara ne da rahotannin jaridu na yanar gizo, waɗanda ba su da sahihanci a matsayin hujja a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa rahoton kafafen yada labarai ba zai iya zama ginshiƙin gaskiya ba, domin ana iya ƙirkirar su ne don cimma wani buri na ƙashin kai, kuma kotu ba za ta rungumi irin wannan gurbatacciyar hanya ba.
“Shigar Ƙarar Marasa Tushe Zai Dagula Tsarin Shari’a”
Mai Shari’a Omotosho ya ce amincewa da irin wannan ƙara da ke cike da rauni da rashin hujja zai buɗe ƙofa ga wasu da dama su riƙa kai ƙara a kotu ba tare da wani sahihin dalili ba, abin da a ƙarshe zai dagula tsarin shari’ar ƙasar.
Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar Diyya
Biyo bayan haka, kotun ta yi watsi da buƙatar diyya ta Naira miliyan 500 da masu ƙara suka nema, tana mai bayyana cewa ba a gabatar da wani sahihin dalili da zai sa kotu ta amince da wannan buƙata ba.
Wannan hukunci ya sake jaddada matsayar kotun tarayya na bin doka da ƙa’ida wajen tantance ƙarar da ake shigarwa, tare da nuna cewa shari’a ba za ta ba da muhalli ga ƙarar da ke dogaro da jita-jita ko rahotannin da ba su da tushe ba.
