Connect with us

News

Gwamnati Ta Haramta Bikin “Signing Out” A Makarantun Firamare Da Sakandare

Published

on

Makaranta

Gwamnatin Jihar Taraba ta haramta duk wani biki ko ɗabi’ar da ta shafi “signing out” da ake yi tsakanin ɗaliban makarantun firamare da sakandare a fadin jihar, tana mai bayyana hakan a matsayin ɗabi’ar da ba ta dace da tsarin tarbiyya da manhajar ilimi ba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Idris A. Goje, ya fitar a ranar Juma’a, inda ya nuna damuwar gwamnati kan yadda ɗaliban makarantun firamare da sakandare ke kwaikwayon ɗaliban manyan makarantu wajen gudanar da bukukuwan “sign out” a lokacin kammala karatu.

Advertisement

Kotu ta yi watsi da ƙarar da Abba Hikima ya shigar a madadin mabaratan Abuja

Sanarwar ta bayyana cewa irin waɗannan bukukuwa da ɗabi’un da ke biyo baya suna barazana ga tarbiyyar ɗalibai, tare da kauce wa tsarin ilimi da aka tsara a matakan farko na karatu.

“A tsarin da Ma’aikatar Ilimi ta tanada, an ware lokaci da hanyoyin da suka dace don mika takardun yaye wa ɗaliban da suka cancanta a matakin karshe. Amma ba wai a gudanar da bukukuwa na kwaikwayo ko na lalata tarbiyya ba,” in ji Goje.

Advertisement

Don haka, Ma’aikatar ta umarci dukkan shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su tabbatar da bin wannan umarni, inda ta jaddada cewa za a dauki matakin ladabtarwa kan duk makarantar da ta karya dokar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su hada kai da gwamnati wajen ganin an kare ɗalibai daga shiga cikin abubuwan da ba su amfanar da su ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending