Connect with us

News

Shugaban Karamar Hukumar Rogo Ya Kaddamar da Kwamitin Raba Takin Gona 

Published

on

Rogo

Rogo

A wani yunkuri na tallafa wa manoma da bunkasa harkar noma a shugaban  karamar hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya kaddamar da kwamitin raba taki mai rangwame ga manoma.

Advertisement

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da Abdu Bako Abdullah Jami’in Yaɗa Labarai, na Karamar Hukumar Rya turawa da Jaridar INDA RANKA

An kafa kwamitin ne domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon buhunan taki 1,800 da za a sayar da su cikin rangwamen kashi 50 bisa 100, kamar yadda gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta tsara.

Advertisement

‎Sudan ta Kudu ta amince da muradun Amurka na jibge fursunonin Venezuela kasarta bayan Najeriya ta yi fatali da bukatar  ‎

Alhaji Abubakar Mustapha Rogo ya bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amana, tare da guje wa duk wani abu da zai jefa tsarin cikin rashin adalci.

Ya kuma bukaci manoma a yankin da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin amfana da wannan damammaki, yana mai jaddada cewa ba a taɓa aiwatar da irin wannan shiri mai amfani a tarihi ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending