Connect with us

News

‎Ƴar Shekara 75 Daga Najeriya Ta Rasu A Wajen Aikin Hajji ‎

Published

on

Hajjin ban
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wata mata mai shekaru 75 da haihuwa daga Jattu Uzairue, a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma, Jihar Edo, ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji a Makkah.

‎Matar mai suna Adizatu Dazumi ta rasu ne a ranar Litinin a Asibitin King Fahad, bayan ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

‎Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Matar Aure ‘Yar Shekara 22 A Kano

‎Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Edo, Alhaji Musah Uduimoh, ne ya tabbatar da rasuwar ga manema labarai a ranar Talata.

‎Ya ce marigayiyar ta fara rashin lafiya ne bayan ta kammala Dawafi a Ka’aba ranar Lahadi, inda aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.

‎Sai dai duk da kokarin da likitoci suka yi, Allah Ya karɓi rayuwarta da safiyar Litinin.

‎An yi jana’izarta kuma aka birne ta a Makkah a ranar da ta rasu, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Advertisement

‎Uduimoh ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kula da lafiyar sauran alhazan da ke cikin kasa mai tsarki.

‎

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending