Connect with us

News

Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Matar Aure ‘Yar Shekara 22 A Kano

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cafke wani mutum da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata matar aure mai shekaru 22, Rumaisa Haruna, a unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke karamar hukumar Kumbotso, Kano.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Talata,  inda ya ce binciken da rundunar ta gudanar ta hanyar dabarun bincike na zamani da amfani da bayanan sirri ne ya kai ga cafke wanda ake zargi.

Advertisement

Kotun  Ta Yanke Wa Wani Magidanci Mai Shekaru 56 Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai

Wanda ake zargin, Shu’aibu Abdulkadir, mai shekaru 35 daga unguwar Madatai, an kama shi ne a ranar 23 ga Mayu, 2025, inda ya amsa laifin shiga gidan marigayiyar ba tare da izini ba, sannan ya shake ta tare da soka mata wuka a wuya har ta mutu.

“Bayan kisan, mijin marigayiyar, Ibrahim Mohammed, ne ya dawo gida ya tarar da matarsa cikin jini. An garzaya da ita zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta,” in ji Kiyawa.

Advertisement

Kakakin ya ce an riga an fara shirin gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala cikakken bincike, kuma yana ci gaba da ba da hadin kai ga jami’an bincike domin gano dukkan masu hannu a lamarin.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa jami’ansa bisa jajircewa da kwarewa da suka nuna a binciken, tare da bukatar al’umma su ci gaba da ba da hadin kai wajen bayar da rahoton duk wani abu da zai iya tayar da zaune tsaye a cikin al’umma.

Advertisement

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending