Connect with us

News

Ana fargabar wata mata ta rataye kanta ta bar jariri mai wata hudu a duniya

Published

on

 

 

Advertisement

Ana fargabar wata matar aure mai ’ya’ya tara ta rataye kanta ta bar jariri mai wata hudu a duniya a Jihar Borno.

 

Advertisement

Gab da Magaribar ranar Asabar ce aka tsinci gawar mai jegon a rataye a cikin gida ta bar jaririn nata a gefe, a unguwar Sajeri da ke gundumar Gumari a Karamar Hukumar Jere ta jihar.

 

Advertisement

Girgizar ƙasar Turkiyya da Syria: Sama da mutum 28,000 sun mutu

 

Wani ganau, Baa Modu, ya ce mijin matar da ’ya’yan ba sa gida a lokacin da abin ya faru, ’ya’yan ne suka fara dawowa suka iske gawarta a rataye a cikin gida.

Advertisement

 

Baa Modua ya ce, ’ya’yan ne suka fito suka sanar da jama’a abin da suka gani, “Da muka shiga mun samu babban dan ya samu ya yanke igiyar, gawar tana kwance a kasa, a gefen ta kuma ga jaririnta mai wata hudu.”

Advertisement

 

 

Advertisement

Ya ce ba a samu wata takarda da ke nuna dalilin abin da ake zargin ta aikata ba.

 

Advertisement

Amma wani ganau kuma makusancin iyalin ya ce matakin da ake zargin matar ta dauka, wuce gona da iri ne, saboda rashin jin dadinta kan sauya gidansu da suka yi.

 

Advertisement

Ya ce, “Danta ya bayyana cewa ba ta so dawowarsu gidan na ba, bayan da aka tashe su daga tsohon gidansu da ke Bulunkutu Kasuwa.

 

Advertisement

“Don ta nuna bacin rantam sai ta kwashe kayanta ta koma gidan iyayenta; sai jiya aka dawo da ita, ba wanda ya san abin da zai biyo baya ke nan.”

 

Advertisement

 

Kokarin wakilin aminiya na samun mijin matar ko jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Borno, Muhammad Shatambaya, kan wannan lamari dai bai yi nasara ba.

Advertisement

 

Domin kuwa har muka kammala haɗa wannan rahoton, kakakin’yan sandan bai amsa kiran waya ba.

Advertisement

 

Shi kuma mijin, ya tafi kai wa ’yan sanda rahoto, amma bai dawo ba, kuma ba a same shi a waya ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending