News
Farfesa Gwarzo Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Marigayin Jarumin Ƙasa Ne
Shugaban Jami’o’in Maryam Abacha da ke Kano da Jamhuriyar Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin babban gibi da kasar da nahiyar Afirka suka yi a tarihin shugabanci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Farfesa Gwarzo ya mika sakon ta’aziyyarsa cikin alhini ga iyalan marigayin, al’ummar Daura, da daukacin ‘yan Najeriya, yana mai cewa Buhari mutum ne da ya rayu da gaskiya, rikon amana da tsantsar kishin kasa.
ADG Care Foundation Zata Yaye Daliban Farko a Shirin ta na Horas da Matasa 650 a Najeriya
“Shugaba Muhammadu Buhari ba kawai jagora ba ne, alama ce ta sadaukarwa, rayuwa mai sauƙi da soyayya ga Najeriya. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa kasa da al’umma tun daga soji har zuwa siyasa,” in ji Farfesa Gwarzo.
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga Disamba, 1942 a Daura, Jihar Katsina. Ya fara mulki ne a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, kafin daga bisani a 2015 ya dawo mulki a matsayin zababben shugaban kasa. Ya kammala wa’adin mulki na shekaru takwas a shekarar 2023.
Farfesa Gwarzo ya ce, koda yake wasu sun saba da manufofinsa, shugabancin Buhari na cike da jajircewa, gaskiya da kyakkyawar niyya ta ganin Najeriya ta samu ci gaba.
“Rayuwarsa ta kasance cike da ƙalubale da nasarori, daga fagen soja zuwa siyasa. Wannan ya nuna yadda ya ke da ƙwazon cika nauyin da ya rataya a wuyansa a madadin al’umma,” in ji Gwarzo.
Ya kara da cewa Buhari ya bar gado mai ƙima na yaki da cin hanci, ƙarfafa tsaro, da gina manyan ayyuka duk da wahalhalu da suka dabaibaye gwamnatinsa.
“Rasuwarsa na nuna ƙarshen wani babi a tarihin Najeriya. Amma darussan rayuwarsa da dabi’unsa za su ci gaba da ba da haske ga masu mulki da al’umma baki ɗaya.”
Farfesa Gwarzo ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin da rahama, ya kuma bai wa iyalansa da ‘yan kasa gaba ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi.
“A irin wannan lokaci, muna tuna cewa shugabanci na gaskiya yana cikin sadaukar da kai da rayuwa mai ma’ana ga kasa. Wannan shi ne Buhari, kuma tarihi ba zai manta da shi ba.”
Yayin da ake ci gaba da samun sakonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na cikin gida da kasashen waje, tarihin Buhari na zaman bawan kasa mai tawali’u da kishin kasa zai ci gaba da rayuwa a zukatan ‘yan Najeriya.
Allah ya jikansa da rahama, ya sanya Aljanna ce makomarsa.
