News
Akalla Kauyuka Biyar Ne Suka Tsere Daga Gidajensu Sakamakon Harin Ƴan Bindiga A Neja
Akalla kauyuka biyar da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja sun shiga halin ɗimuwa, bayan wani mummunan hari da ƴan bindiga suka kai da safiyar Litinin, lamarin da ya tilasta mazauna yankin tserewa daga gidajensu don neman mafaka.
Kauyukan da harin ya fi shafa sun haɗa da Ya-Bawa, Maburya, Ragada, Kura’a da Kumbashi, inda aka ce maharan sun shigo cikin tarin jama’a dauke da muggan makamai, suna harbe-harbe ba kakkautawa.
Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Gagarumin Shiri Don Dakile Matsalar Kwacen Waya Da Fadan Daba
Wani mazaunin ƙauyen Ya-Bawa ya shaida wa manema labarai cewa, “Ƴan bindigar sun mamaye ƙauyukan cikin safiya, mun hango su daga tsauni – fiye da mutum 200, kowannensu na kan babur – sai muka tsere kafin su iso.
Bayan kammala farmakin Mariga, majiya daga yankin ta ce maharan sun zarce zuwa Rijau – hedikwatar karamar hukumar Rijau – inda suka kutsa cikin garin da misalin ƙarfe biyu na rana, suka kuma yi garkuwa da mutane da dama.
Wani shaidar gani da ido daga Rijau mai suna Bilya ya bayyana cewa: “Sun shigo Rijau ba tare da wani gargadi ba, kuma sun tafi da mutane da dama har da wadanda ke ƙoƙarin gudu.”
Wasu daga cikin waɗanda suka tsere daga garuruwan sun bayyana cewa ba su samu damar ɗauko komai daga gidajensu ba, ciki har da kayan abinci, lamarin da ya bar su cikin mawuyacin hali har zuwa yammacin Litinin.
Da aka tuntube shi, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Manjo Janar Bello Abdullahi (mai ritaya), ya tabbatar da faruwar harin. Ya ce gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace don dakile barazanar tare da dawo da doka da oda a yankunan da abin ya shafa.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin hana ci gaba da kai hare-hare tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
