News
Matashi Ya Nemi Shugabannin Najeriya Su Saurari Saƙonsa Kan Makomar Al’umma
Wani matashi ɗan Najeriya, Isa Abdullahi Gwamya, ya bayyana cewa yana ɗauke da saƙo mai matuƙar muhimmanci da ya shafi makomar al’umma, wanda ya ce ya shafe lokaci yana addu’a da nazari kafin ya yanke shawarar bayyana shi ga duniya.
Isa, wanda shi ne ya kafa ƙungiyar NIU Future of Humanity, ya bayyana cewa saƙon nasa ya shafi muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai, adalci da tsoron Allah, wanda ya ce yana da amfani ga ɗaukacin bil’adama – ba kawai a Najeriya ko Afirka ba, har da duniya gaba ɗaya.
Shugaba Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Muhammadu Buhari University
A cikin wani saƙo da ya fitar ta kafafen sada zumunta a ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025, Isa ya ce:
“Na dade ina tunanin wannan saƙo. Na gaji da ɓoye shi a raina. Na yanke shawarar bayyana shi domin na tabbata yana da amfani ga al’umma.”
Matashin ya ce tuni ya kai wasiƙun da ke ɗauke da wannan saƙo zuwa wurare da dama da suka haɗa da Ofisoshin ‘yan sanda biyu a Kano, Babbar Kotun Tarayya, Gidajen rediyo, Da kuma Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II
Isa ya ce ya ɗauki wannan mataki ne da fatan saƙon zai isa ga shugaban ƙasa, masu tsara manufofi da shugabannin addinai. Sai dai, ya ce har yanzu bai samu wani martani ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar fitar da saƙon ta hanyar kafafen sada zumunta.
>L“Na rubuta wannan hangen nesa a cikin wani littafi. Na tattauna da mutane da dama, kuma yawancin su sun amince cewa saƙon zai amfani duniya,” in ji shi.
Duk da cewa ba sananne ba ne a idon jama’a, Isa ya ce yana da ƙwarin gwiwa cewa duniya na buƙatar sauraron irin wannan saƙo, musamman a wannan lokaci da duniya ke fuskantar matsaloli da dama.
Ya kuma yi kira ga kafafen watsa labarai da su bashi dama domin ya gabatar da cikakken bayani game da wannan saƙo.
A ƙarshe, ya bayyana cewa wayarsa za ta ci gaba da kasancewa a buɗe domin duk wanda ke da buƙatar jin karin bayani: 08127008857.
