Connect with us

News

INEC Za Ta Bai Wa Fursunoni Damar Kada Ƙuri’a A Lokacin Zaɓe

Published

on

INEC Yakubu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa daga yanzu, fursunonin da ke gidajen gyaran hali a Najeriya za su samu damar yin rajista da kada ƙuri’a a dukkan zaɓuɓɓuka.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin karɓar bakuncin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa, Sylvester Nwakuche, a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Advertisement

Gwamnoni 29 Sun Kashe Naira Biliyan 80 Kan Tafiye-Tafiye A Cikin Wata Shida

Yakubu ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke, wanda ya tabbatar da cewa ɗaurarru na da cikakken ‘yanci na yin rajista da kada ƙuri’a kamar sauran ‘yan ƙasa.

A cewarsa, hukumar za ta yi aiki tare da hukumar kula da gidajen yarin domin tsara yadda fursunonin za su kada ƙuri’a, ciki har da samar da damar gudanar da zaɓe a cikin gidajen gyaran hali ko wuraren da suka dace.

Advertisement

Ya kuma nemi haɗin gwiwar majalisar dokokin ƙasa wajen samar da ƙudurin doka da zai ƙarfafa wannan sabon tsari.

A nasa jawabin, Nwakuche ya bayyana cewa akwai sama da fursunoni 81,000 a faɗin ƙasar, kuma kusan kashi 66 cikin ɗari daga cikinsu na jiran shari’a ne, ba tare da an yanke musu hukunci ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending