News
Gwamnatin Kano za ta kashe Naira Biliyan 14.8 domin gudanar da manyan ayyuka
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 14.8 domin aiwatar da manyan ayyuka a fannoni daban-daban na raya jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Ibrahim Waiya, ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan zaman majalisar a ranar Juma’a.
INEC Za Ta Bai Wa Fursunoni Damar Kada Ƙuri’a A Lokacin Zaɓe
A cewar Kwamishinan, daga cikin kudaden da aka amince da su:
Naira miliyan 364 za a kashe wajen gyaran Asibitin Haihuwa na Sabo Bakin Zuwo da ke unguwar Jakara.
Naira miliyan 294 za a yi amfani da su wajen gyaran manyan gine-gine a Makarantar Koyar da Fasahar Lafiya ta Bebeji.
Naira miliyan 113 za a ware don girka na’urorin hasken rana a asibitocin haihuwa guda biyar a fadin jihar.
Sama da Naira miliyan 112 za a kashe wajen samar da magunguna da kayan aiki a Asibitocin Hasiya Bayero, Murtala Muhammad da Yadakunya.
Naira miliyan 272 za a yi amfani da su wajen gyara da sabunta wani gida da aka saya a unguwar Zango domin amfanin Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.
Naira miliyan 128 za su tafi wajen samar da kayan aiki ga dakunan asibiti guda biyu da aka gyara a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.
Naira miliyan 379 za a kashe wajen gyaran ginin cibiyar kiwon lafiya ta farko a Zakirai tare da ƙara sabon gini a wurin.
Naira miliyan 169 za a ware domin gyaran ƙananan madatsun ruwa guda biyar a Madobi, Gwarzo, Garun Malam, Kibiya da Ajingi.
Waiya ya bayyana cewa matakan sun zama wajibi domin tabbatar da ci gaban al’umma, musamman a fannin kiwon lafiya, ilimi da samar da ababen more rayuwa a dukkan sassan jihar.
