News
Mun Yi Kuskure’: WAEC Ta Fadi Abin Da Ya Jawo Dalibai Suka Fadi Jarabawar 2025
Hukumar WAEC ta tabbatar da cewa ta samu kuskure a sakamakon jarabawar SSCE na 2025 da ta fitar a farkon mako.
Sabbin bayanai sun nuna cewa yanzu dalibai 1,239,884 (kashi 62.9%) ne suka samu nasara a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, maimakon kashi 38.32% da aka sanar da farko.
Gwamnatin Kano za ta kashe Naira Biliyan 14.8 domin gudanar da manyan ayyuka
Shugaban WAEC a Najeriya, Dr. Amos Dangut, ya ce an samu matsala wajen buga tambayoyin Turanci na “objective” inda aka yi amfani da mabuɗin amsa mara daidai, wanda ya shafi daliban da suka yi jarabawar a takarda kawai.
An gyara kuskuren kuma sabbin sakamakon suna samuwa a shafin hukumar www.waecdirect.org.
Cikin waɗanda suka yi nasara akwai 582,065 maza da 657,819 mata.
Duk da haka, an samu raguwar wadanda suka yi nasara a bana da kashi 9.16% idan aka kwatanta da sakamakon 2024.
WAEC ta nemi afuwar dalibai, iyaye da malamai, tare da alkawarin cewa za ta ɗauki matakan hana irin wannan kuskure a nan gaba.
