Connect with us

News

Makarantar Al’mumtaz Academy Keffi Za Ta Gudanar da Ranar Jawabi da ba da Kyaututtuka ta 2025- Inji Dr. Musa Ahmad Isa

Published

on

IMG 20250809 WA0045
Advertisements
ads

DAGA JOHN D. WADA, Keffi

Makarantar Al’mumtaz Academy dake Keffi jihar Nasarawa za ta gudanar da Ranar Jawabi na musamman da ba da kyaututtuka ta 2025.

Acewar daraktan makarantar Dr. Musa Ahmad Isa, makarantar ta kammala shirye-shiryen gudanar da wannan taron ne wadda take gudanar shekara-shekara a ranar Lahadi, 10 ga watan Agusta, 2025 a babban filin taron Jami’ar Jihar da ke Keffi.

2027: ADC Tana Farautar Jigo a Jam’iyyar APC Domin Ya Tsaya Mata Takarar Gwamana A Kaduna 

Dr. Musa Ahmad Isa ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da ya yi da ‘yan jarida a ofishinsa da ke cikin ginin makarantar a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025.

Acewar sa wannan taron mai dinbin tarihi zai baiwa daliban makarantar damar nuna basiraran su da kwarewarsu da kuma hankalinsu ta hanyar gabatar da jawabai da wasan kwaikwayo dabandaban da nufin ilmantar da jama’a kan rayuwar yau da kullum, matsaloli, da kuma hanyoyin magance su.

Daraktan ya kuma bayyana cewa taron zai kunshi ayyuka na musamman, da suka hada da wasan kwaikwayon mai suna “The Headteacher,” a turance da tsarin haddar Alkur’ani/Khatma, da kuma bayar da lambobin yabo da tallafin karatu ga wasu daliban (Nursery, Primary, JSS, da SSS).

Advertisement

Sa’anan za a kuma karrama wasu manyan sarakuna da ‘yan siyasa musamman maimartaba sarkin Keffi, alhaji Shehu Chindo Yamisa na III da sanata Aliyu Wadada da lambobin yabo na musamman da sauran su duk a lokacin taron.

Dr. Musa Ahmad akarshe ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da iyayen yara da gwamnatoti a duka matakai su bai wa mahukuntar makarantar hadin kai kafin, a lokacin, da kuma bayan taron, domin baiwa makarantar damar ci gaba da samar da ilimi mai inganci wa al’umma baki daya.

Al’mumtaz Academy Keffi dai ba shakka tana da tarihi na musamman na samun nasarori tun daga kafuwarta kuma an san ta da horar da shugabannin manyan gone da suka yi fice a fannin ilimi da hankali da al’ada da kuma uwa uba addini da ilimin zamani wanda ke cigaba da taimakawa ga jin dadin al’umma baki daya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending