Connect with us

News

Cikakken Tsarin Kananan Gwamnatoci Ne Mafita Ga Matsalolin Najeriya —Farfesa Gidado

Published

on

IMG 20250809 WA0002
Advertisements
ads

‎DAGA JOHN D. WADA, LAFIYA 

Wani sanannen farfesan Sheri’ar doka wato Constitutional Law a turance dake sashin karatun Sheri’a ta babban jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi a jihar farfesa Maxwell Michael Gidado yace babbar hanyar tabbatar da cigaba mai daurewa a qasar nan ta Najeriya baki daya shine ta kirkiro da wani tsarin kananan gwamnatoti wadda zasu yi aikin su ne batare da sa bakin babbar gwamnatin qasar ta tsakiya ba wato Federal government a turance ba kamar yadda lamarin yake a yanzu.

Farfesan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wani lacca na musamman karo na 53 wadda jami’ar ke shirya aka gudanar a babban dakin taron jami’ar a mako da ake ciki.

Cikakken Tsarin Kananan Gwamnatoci Ne Mafita Ga Matsalolin Najeriya —Farfesa Gidado

Acewar sa a kimanin sama da shekaru 40 da yayi a matsayin malamin Sheri’a har yakai matsayin farfesa da mai bincike na musamman da sauran su tuni ya gano cewar kirkiro da kananan gwamnatotin masu aiki da gaske ta fannin sheri’ar shine babbar mafita ga dinbin matsaloli musamman ta tattalin arziki da ake fuskanta a yanzu.

Babban farfesan sheri’an ta babban jami’ar jihar Nasarawa farfesa Maxwell Michael Gidado ya kuma jaddada cewar a hukumance za a iya cewa Najeriya na aiwatar da shugabancin tsakiya da kanana ne amma a zahirance akasin haka ake gudanar wato gwamnati daya tilo ne da ake kira Unitary system of government maimakon Federal system of government a turance.

Ya cigaba da bayyana cewa “A tsarin kananan gwamnatotin da nake nufi ko wacce jiha zata samu nata fifiko ne ta kuma rika gudanar da shugabancin ta kai tsaye da cin gashin kan ta a duka matakai batare da sa baki ko idon babbar gwamnatin ta sama ba.” Inji shi.

Advertisement

Farfesa Maxwell Michael Gidado ya kara da cewa a tsarin har ila yau baza a fuskanci yawan korafe-korafe da zargin bangaranci da sauran su kamar yadda ake fuskanta daga wasu sassan qasar nan a yanzu ba kana a kuma samu dinbin nasarorin a yankunan karkara.

Sai dai duk da hakan farfesan ya kuma bayyana cewa baza a rasa wasu kananan kalubalai ba a sabon tsarin da yake baida shawarar musamman kamar yin amfani da hukumomin tsaro a kananan gwamnatotin wajen cimma burin zuciya da wasu shugabannin zasu yi da rashin nuna adalci da sauran su inda ya shawarci a tabbatar an gudanar da cikakken karin bincike kafin a kirkiro tareda aiwatar da tsarin.

Anata bangare da take jawabi a wajen laccar shugabar jami’ar farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta jaddada mahimmancin laccar na musamman da ake gudanar a jami’ar akai-akai wadda tace kan bai da dama wa su farfesan jami’ar su amfanar da al’umma baki daya daga dinbin basirorin su da kwarewan su don inganta al’umma dama qasa baki daya.

Ta yaba wa farfesa Maxwell Michael Gidado dangane da sadakarwa da aiki tukutu da yake yi a jami’ar ta gina dalibai a fannin ta sheri’a inda tace tabbas farfesan daya ne daga cikin farfesoshin da jami’ar ke cigaba da yin alfa’ari dasu kana tace ba shakka taken laccar ya zo dai dai da lokacin kuncin rayuwa da ake fuskanta a qasar kuma laccar zai taimaka wajen dawo da martaban shugabanci a duka matakai a qasar nan.

Akarshe sauran manyan baki da suka halarci laccar da suka hada da tsohuwar ministar harkokin mata na Najeriya Dame Pauline Tallen da dokta Sulaiman Nchi daga fannin karatun sheri’ar ta jami’ar da sanata Dino Malaye da sarakunan gargajiya da sauran su duk sun yaba wa farfesan inda suka yi kira ayi amfani da wadannan ingantattun shawarwari daya aiyana a laccar na musamman.

Daga bisani shugabar jami’ar farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta gabatar wa farfesa Maxwell lambar yaba na musamman inda aka kuma dauka hotuna da sauran su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending