Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Sallami Masu Taimaka Masa Biyu Bisa Hannu A Belin Danwawu, Da Karkatar Da Tallafi

Published

on

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami Babban Mai Taimaka masa a Ofishin Sakataren Gwamnati, Hon. Tasi’u Adamu Roba, da wani hadiminsa kan zarge-zargen karkatar da kayan tallafi da kuma hannu a belin Sulaiman Danwawu, wanda ake zargin yana da alaka da miyagun kwayoyi.

Sanarwar korar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Yaɗa Labaran Sakataren Gwamnatin Kano, Musa Tanko Muhammad, a ranar Asabar.

Advertisement

Trump Zai Gana Da Putin a Birnin Alaska

Sanarwar kara da cewa , dama an riga an gurfanar da Tasi’u Roba gaban kotu kan zargin karkatar da buhuhunan kayan tallafin abinci na palliative, tare da chanja sunayen wadanda aka yi wa rajista domin amfana da tallafin.

Bayan rahoton da kwamitin bincike na musamman ya gabatar, Gwamna Abba ya tabbatar da sallamarsu daga aiki, tare da gargadin cewa kada su sake bayyana kansu a matsayin jami’an gwamnatin Kano mai ci yanzu.

Advertisement

Sanarwar ta kuma umarci Tasi’u Roba da ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa daga yau zuwa ranar Litinin.

Rahoton kwamitin ya nuna cewa hadimin na da hannu wajen shirya yadda aka karɓi belin Danwawu, lamarin da gwamnatin Kano ta bayyana a matsayin saba ka’ida da kuma karya doka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending