News
An Cafke Wani Fitaccen Dilan Ƙwaya a Kano
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta ce ta cafke wani matashi da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a yankin Fagge na jihar Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya shaida a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi cewa an kama wanda ake zargin, Faisal Yusuf Umar, mai shekaru 23, ne bayan wani bincike da aka gudanar bisa bayanan da al’umma suka bayar.
Maigatari ya ce jami’an NDLEA na reshen Fagge sun kai samame a ranar 18 ga watan Yuli a gidan wanda ake zargin da ke unguwar Dandali, inda suka gano kwalabe 40 na maganin tari Benylin mai ɗauke da Codeine (kimanin kilo 4), da kuma kuɗi naira 204,000 da ake zargin sun fito daga saida miyagun ƙwayoyin.
Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
