Connect with us

News

Mutane Da Dama Sun Mutu A Wani Sabon Haɗarin Kwale-kwale A Sokoto

Published

on

IMG 20240813 WA0007 (1)

An sake samun wani mummunan haɗarin kwale-kwale a jihar Sokoto, bayan wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kife a yankin ƙaramar hukumar Shagari ranar Alhamis, lamarin da ake fargabar ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, yayin da wasu kuma ake ci gaba da nema.

Leadership ta rawaito, Mai ba wa Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Aminu Liman Bodinga, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa wannan shi ne karo na uku da irin wannan hatsari ke faruwa a jihar cikin wata guda.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa Malamin Islamiyya Daurin Shekara 21 A Gidan Gyaran Hali A Kano 

Ya ce hukumar SEMA tare da NEMA da kuma NIWA sun tura jami’an ceto zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto da kuma ɗebo gawawwaki.

 

Advertisement

Shaidu sun bayyana cewa kwale-kwalen da ya kife yayin da ya ke cike da maza, mata da yara, kafin ya nutse a tsakiyar hanya, lamarin da ya jefa fasinjojin cikin ruwa. Wasu sun yi nasarar yin iyo suka tsira, amma da dama har yanzu babu labarinsu.

Al’ummar yankin sun ce matsalar yawan cike jirgin ruwa, rashin amfani da lif-jacket, da kuma rashin bin dokokin tsaro ne ke jawo aukuwar irin wadannan hadurra.

Advertisement

Mutanen yankunan da ke dogaro da ruwa wajen zirga-zirga da gudanar da harkokin yau da kullum na cikin fargaba da bakin ciki, yayin da iyalai da dama ke jiran labari kan makomar ƴan uwansu da suka bata.

Wannan hatsari ya sake tayar da hankali kan bukatar gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da kyakkyawan yanayi a hanyoyin ruwa, domin kare rayukan al’umma

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending