News
Yadda Manoma Ke Fuskantar Gagarumin Ƙalubale A Lokacin Damuna A Najeriya
A duk lokacin damuna, al’ummar karkara a Najeriya, musamman manoma, na ci gaba da fuskantar matsaloli masu tsanani sakamakon rashin hanyoyin mota, gadoji da kuma rashin ingantaccen tsari na tallafa wa harkar noma.
Duk da cewa manoma a karkara ke samar da kaso mafi tsoka na kayan abincin da ake amfani da shi a birane, rahotanni sun nuna cewa rashin hanyoyi na jefa su cikin ƙalubale na kai amfanin gonakinsu kasuwanni. Wannan matsala na haddasa asara mai yawa ga manoma, yayin da tattalin arzikin ƙasa ke fuskantar koma baya sakamakon durkushewar harkar noma a wasu sassan ƙasar.
Mutane Da Dama Sun Mutu A Wani Sabon Haɗarin Kwale-kwale A Sokoto
A wasu yankuna, lalacewar hanyoyi da kwararar ruwa ke haddasawa a lokacin damuna ya jawo katse hulɗar kasuwanci, lamarin da ke sa kayayyakin abinci su yi tsada a birane. Manoma na korafi cewa rashin kayan aikin noma na zamani da tallafi daga gwamnati ya kara jefa su cikin wahala, inda da dama ke noman kananan fili ba tare da samun riba ba.
Wasu shugabannin al’umma a karkara sun bayyana damuwarsu kan yadda gwamnati ke ci gaba da nuna halin ko-in-kula, duk kuwa da cewa harkar noma ita ce ginshikin tattalin arzikin Najeriya. Sun ce wannan gazawa na kara haifar da talauci da barazanar tsaro a wasu yankunan karkara, tare da sa matasa barin gona don neman rayuwa a birane.
Masu sharhi kan tattalin arziki sun bukaci gwamnati da ta sanya gyaran hanyoyi da gadoji cikin ajandar ta na ci gaban kasa, tare da samar da kayan aikin noma na zamani da tallafin manoma. Sun ce hakan zai taimaka wajen bunkasa harkar noma, rage tsadar abinci, da kuma karfafa tattalin arzikin kasa baki daya.
A halin yanzu, damuna na ci gaba da jefa manoma cikin matsaloli, lamarin da ke kara bayyana gibin dake tsakanin karkara da birane a Najeriya.
