Connect with us

News

GADAR ƘAUYEN KUREKEN SANI TA RUSHE: Dubban Mutane Sun Makale, Al’umma Na Roƙon Matakin Gaggawa Daga Gwamna Yusuf

Published

on

IMG 20250909 WA0011
GADAR ƘAUYEN KUREKEN SANI DA TA RUSHE

Wata gada da ake kira Gadar Dare da ke ƙauyen Kureken Sani, a cikin al’ummar Danshana ta ƙaramar hukumar Kumbotso, Jihar Kano, ta rushe bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a daren Litinin.

Gadar, wadda ta dade tana zama hanyar haɗin al’ummar Yanshana da Naibawa, ita ce ginshiƙin zirga-zirgar yau da kullum na mazauna yankin wajen zuwa kasuwanni, makarantu da kuma jigilar marasa lafiya zuwa asibitoci. Rushewar gadar ya jefa dubban jama’a cikin mawuyacin hali.

Majalisa Ta Hana Sanata Natasha Komawa Aiki Duk Da Cikar Watanni 6 Na Dakatarwa

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema Labarai cewa, al’ummar da ke amfani da gadar sun makale, lamarin da ya ƙara tsananta musu rayuwa.

“Dalibai, marasa lafiya, ‘yan kasuwa da ma’aikata sun shiga wahala. Hanyar da ake bi yanzu tana da tsawo ƙwarai, tana ɗaukar kilomitoci masu yawa kafin a kai inda ake so,” in ji shi.

Ya ce tun daɗewa gadar ta fara nuna alamun rauni, amma duk da haka ba a ɗauki wani mataki na gyara ba, har sai da ta rushe baki ɗaya. Sai dai ya nuna godiya ga Allah cewa babu wanda ya rasa ransa, kasancewar lamarin ya faru ne da dare lokacin da ba a cika zirga-zirga a kan gadar ba.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa sun fara shirin garzayawa gidan gwamnatin Jihar Kano domin mika koke da neman matakin gaggawa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman ganin cewa gadar na da matuƙar muhimmanci ga rayuwarsu ta yau da kullum.

Advertisement

A halin da ake ciki, an gargadi iyaye da su sa ido sosai kan yaransu domin kada su kusanci wurin da lamarin ya faru kasancewar ruwan sama da ke ci gaba da sauka na iya ƙara janyo haɗari a wajen.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending