News
Uba Ya Maka Saurayin ’Yarsa A Kotu Kan Zargin Satar Kudaden Fensho
Wani uba, Ishaku Joseph, ya gurfanar da saurayin ’yarsa, Yunana Zock, a gaban wata kotu a Kaduna bisa zargin satar kudaden fanshon matarsa da ta rasu, da suka kai sama da naira miliyan 13.
Lauyan gwamnati, Jeremiah Amfani, ya bayyana cewa kudaden an tura su ne zuwa asusun Emmanuella, ’yar Joseph, a shekarar 2023 kasancewar ita aka nada a matsayin magajiya. A cewarsa, wanda ake tuhuma ya yaudari budurwarsa ya kuma kwashe dukkan kudaden daga asusun ba bisa doka ba.
A lokacin da take ba da shaida a gaban kotu, Emmanuella ta tabbatar da cewa saurayinta ya sace katin ATM ɗinta ba tare da saninta ba, sannan ya cire kudaden gaba ɗaya.
Sai dai a martaninsa, Yunana ya musanta zargin, inda ya ce ya karɓi kudaden ne da yardar budurwarsa. Ya bayyana cewa Emmanuella ta amince za ta ba shi naira miliyan biyu domin ya fara kasuwanci. A cewarsa, sun shafe lokaci tare a Abuja kuma sun musayar da juna lambobin sirrin ATM.
Yunana ya kuma gabatar da bayanin asusun Opay ɗinsa a matsayin hujja, tare da ikirarin cewa zai kawo wani shaida a zaman gaba.
Mai shari’a, Patience Musa, ta dage zaman shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraron karar.
