Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Ƴan jarida A yobe, Sun Harbe Ɗan Sanda

Published

on

Ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari kan Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe, inda suka harbi ɗan sanda guda ɗaya a wajen da safiyar Juma’a.

Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 2:00 na asuba, ranar 19 ga Satumba, 2025, a Damaturu, babban birnin jihar.

Advertisement

Stallion Times Ta Mika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwar Sarkin Gabas, Idris Adamu Dankabo

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta kan ɗan sandan da ke tsaron harabar sakatariyar, inda harsashi ya same shi a ƙafa. An garzaya da shi Asibitin ƴan sanda na Damaturu inda yake karɓar magani a halin yanzu.

Shugaban ƙungiyar NUJ reshen Yobe, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin “takaici da tsoratarwa” ga ƴan jarida da ke gudanar da aikinsu cikin mawuyacin hali.

Advertisement

“Harin nan ba wai kan ɗan sanda kaɗai aka kai shi ba, illa da barazana ce ga dukkanin ƴan jarida a jihar Yobe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Muna kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi, tare da tabbatar da cewa an cafke waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki domin fuskantar hukunci.”

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending