News
Masar Ta Gano Ɓarayin Munduwar Fir’auna Da Suka Narka Tare Da Sayar Da Ita
Hukumomin Masar sun ce sun gano ɓarayin munduwar zinariya ta Fir’auna mai tarihi wadda aka sace daga gidan tarihin ƙasar a birnin Alkahira, inda daga baya aka narka ta aka sayar da ita kan kuɗi dala dubu huɗu.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta bayyana cewa munduwar ta kasance mallakin Fir’auna Amenemope, wadda ta kai kimanin shekaru dubu uku . An gano cewa munduwar ta ɓace ne tun ranar 9 ga Satumba, 2025 daga gidan tarihin da ake ajiye ta a Alkahira.
Ma’aikatan FIRS huɗu da na UCP 6 sun rasa rayukansu a gobarar wani babban ofis a Legas
Rahotanni sun nuna cewa wani ƙwararren mai sarrafa kayan tarihi ne ya fara sayar da munduwar ga wani ɗan kasuwar zinariya, wanda daga bisani ya mika ta ga wani mai shago da ya shahara a harkar kayan ado.
Mai shagon ya sake sayar da ita ga wani mai aikin narkar da zinariya, wanda ya narka munduwar ya kuma sauya fasalinta gaba ɗaya.
Hukumomin Masar sun ce wannan munduwa na daga cikin manyan kayayyakin tarihi da ake shirin kaiwa baje-kolin tarihi a Italiya a watan gobe kafin a sace ta.
Tun farko dai an kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike da kuma kai samame a faɗin ƙasar domin gano kayan tarihi da suka ɓace daga gidan tarihin.
