News
Mutane Sama Da 150 Sun Mutu Sakamakon Haɗururruka A Wuraren Gine-gine A Najeriya
Hukumar Kula da Inshorar Al’umma a Najeriya (NSITF) ta nuna damuwarta kan mutuwar mutane sama da 150 sakamakon Haɗururruka a wuraren gine-gine a shekarar 2024.
Manajan daraktan hukumar, Oluwaseun Faleye, ya bayyana haka ne a taron shekara na 69 na ƙungiyar masu aikin gine-gine ta ƙasa (Federation of Construction Industry) da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
Tsananin gudu da kura-kuran matuƙi ne suka janyo faduwar jirgin kasan Abuja-Kaduna —Hukumar NRC
Faleye ya ce Najeriya na fuskantar matsalar haduran gine-gine akai-akai, inda ake samun hatsarori tsakanin 50 zuwa 70 a kowace shekara, ciki har da rushewar gine-gine, faɗuwa daga manyan gine-gine, da raunuka daga amfani da injuna.
“A cewar Hukumar Tsaro ta Najeriya, fiye da mutane 150 ne suka mutu sakamakon Haɗururruka a wuraren gine-gine a shekarar da ta gabata,” in ji shi.
Ya kara da cewa wannan al’amari ya nuna muhimmancin ƙarfafa matakan tsaro da bin ƙa’idojin lafiya a wuraren aiki.
Ya bukaci kamfanonin gine-gine su haɗa kai da NSITF wajen gudanar da bincike, horo da daukar matakan kariya, domin rage Haɗururruka da ake fuskanta a nan gaba.
-
Opinion5 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion5 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
