News
Wani Matashi Ya Kashe Kakanninsa Biyu A Kano
Wani matashi mai suna Muhammad, wanda ke da kimanin shekara 20 da haihuwa, ana zargin ya kashe kakanninsa biyu ta hanyar caka musu wuka a unguwar Kofar Dawanau da ke cikin birnin Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025, kamar yadda wani makocin mamatan, Malam Mukhtar Harisu, ya shaida wa tashar Muhasa TV da Rediyo.
Mutane Sama Da 150 Sun Mutu Sakamakon Haɗururruka A Wuraren Gine-gine A Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya aikata wannan mummunan aiki ne bayan ya yi amfani da miyagun ƙwayoyi, sai dai wasu mazauna yankin sun ce tun da dadewa yana fama da lalurar tabin hankali.
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da Dan Sokoto da kuma Hajiya Tasidi, dukansu mazauna birnin Kano.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da Muhammad ke yi wa kakanninsa barazanar kisa ba, sai dai duk da haka, ba su taba daukar wani mataki a kai ba kafin wannan lamari ya auku.
Kokarin da Jaridar Inda Ranka ta yi na jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba, domin bai amsa kira ko sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
