News
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ake Zargi Da Kashe Kakanninsa A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafewar wani matashi da ake zargi da halaka kakanninsa a Kofar Dawanau, karamar hukumar Dala, ta hanyar caccaka su da wuka.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa matashin mai suna Mutawakilu Ibrahim, dan shekara 30, ya aikata laifin ne sakamakon sabani da kakanninsa suka yi, abin da ya haifar da munanan raunuka har suka yi sanadiyar rasuwar su.
An garzaya da mamatan zuwa Babban Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu. Daga bisani an mika gawar su ga iyalai don yi musu jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.
Binciken farko ya nuna cewa matashin na amfani da miyagun kwayoyi. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin ci gaba da bincike a sashen manyan laifuka kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.
-
Opinion5 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion5 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
