News
Karyewar Gadar Gwangwan Na Kara Janyo Tsaiko Ga Rayuwar Al’umma
Dagacin garin Gwangwan, Malam Muhammad Tukur, ya bayyana damuwarsa kan yadda karyewar gadar shiga garin ke kawo tsaiko ga rayuwar al’umma.
Ya ce, “Da yawa daga cikin jama’a idan ruwa ya yi, basa iya fita daga garin. Wannan yana kawo matsaloli wajen samun lafiya, fitar da amfanin gona, da harkokin ilimi na dalibai.
Gwamna Kano Ya Miƙa Korafe-korafen Kungiyoyin Addini Kan Malam Lawan Triumph Zuwa Ga Majalisar Shura
Malam Tukur ya kara da cewa, saboda lalacewar gadar, “Dole ne idan kazo bakin rapi sai ka biya matasan da suke zaune a wurin domin su fitar da kai da kayan ka,” in ji shi Kamar yanda PREMIER RADIO ta ruwaito
Al’ummar garin Gwangwan da mazaɓun Ruwan Bago, Falgore da Rogo Ruma sun ce lalacewar gadar na janyo hatsari ga mutane, ciki har da mata masu juna biyu, da kuma tabarbarewar harkokin kasuwanci.
Bugu da kari, garin Gwangwan yana fuskantar wasu matsaloli na yau da kullum kamar rashin Asibiti , ƙarancin ababen more rayuwa, da matsalolin hanyoyi. Wadannan kalubale suna kara wahalar da rayuwar al’umma da kuma hana ci gaban kasuwanci da ilimi.
Sakamakon haka, mazauna garin sun roki Gwamnan Kano da ya dauki mataki na gaggawa domin gyara gadar da kuma tallafa wa al’umma wajen shawo kan sauran matsalolin da suke fuskanta.
