News
Ƴansanda Sun Kama Mai-Gadi da Aka Zargi da Satar Yaro Ɗan Shekara Biyu A Legas
Rundunar ƴan sanda na jihar Legas ta damke wani mai-gadi, Amos Kini, bisa zargin satar yaro ɗan shekara biyu a unguwar Elemoro.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar a yau Litinin, ta bayyana cewa mahaifiyar yaron ce ta kai rahoto ga sashen ƴan sanda makon da ya gabata.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:50 na dare, lokacin da mahaifiyar ta kai rahoto cewa ma’aikacin tsaronta ya gudu da ɗanta da wayarta ba tare da izini ba.
Bayan satar, wanda ake zargi ya yi amfani da wayar da ya sace wajen kiran mahaifin yaron, inda ya nemi Naira miliyan biyar (₦5,000,000) a matsayin kuɗin fansa kafin ya saki ɗan.
Haka kuma, rundunar ta kama wani mutum mai suna Aruna Dauda, wanda ya tsaya wa Amos shaida kafin a ɗauke shi aiki, domin gudanar da tambayoyi.
Daga baya, wanda ake zargin ya saki yaron, amma rundunar ta ci gaba da bin sawun shi har sai da aka cafke shi.
“A ranar 23 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, jami’an sashin Tactical Squad (Hyena), bayan samun sahihan bayanai, sun gano inda yake suna kuma suka cafke Amos Kini a unguwar Elemoro. Ya amsa laifinsa, yanzu yana hannun ‘yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike,” in ji Adebisi.
