Connect with us

News

Jami’an Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano

Published

on

Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro.

Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro.

Advertisement

CSADI Ta Tallafawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 400 Da Abinci Mai Gina Jiki A Kano

Rahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ’yan sanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru.

Wata majiya ta ce, yayin da bindigarsa ƙirar AK-47 ke rataye a wuyansa, sai ya matsa kunamar bindigar bisa kuskure.

Advertisement

“An samu bindigar, mai lambar rajista GT 4177, tare da harsashi ɗaya da aka harba. An lissafa harsashi 29 daga cikin 30 da aka ba shi,” in ji majiyar.

An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Advertisement

An ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin domin yin bincike.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa har yanzu ana bincike kan lamarin, kuma za su bayyana sakamakon nan gaba.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending