Connect with us

News

Yadda Wani Matashin Malamin Addinin  Ya Mutu A Hannun ‘Yan Sanda A Kano

Published

on

Unguwa gawa

Iyalan wani malamin addinin Musulunci a Kano, sun koka kan yadda ya rasu a hannun ‘yan sanda bayan sun azabtar da shi.

Salim Usman, wanda limami ne a a unguwar Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a cikin garin Kano ya rasu ne a yayin da yake tsare a sashen yaƙi da manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda ta Kano a ranar Litinin.

Advertisement

Jami’an Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano

Wasu jami’an rundunar ‘yan sanda ne suka je har gidan su Imam da ke unguwar Forestry a Kuntau da misalin ƙarfe 7 na dare a ranar Litinin bayan ya kammala sallar Magariba.

Jami’an sun ce akwai wani mutum da suka kama wanda ake zargi da satar buhun fulawa a bara wanda ya ambaci matashin malamin mai shekara 24 da wanda ya sayi buyin fulawar.

Advertisement

Hotunan bidiyon CCTV da wannan jarida ta gani sun nuna yadda ‘yan sanda suke dukan Usman bayan sun kama shi.

A bidiyon an ga jami’ai biyu – ɗaya cikin kayan sarki riƙe da bindiga a yayin da ɗayen ke sanye da kayan gida.

Advertisement

Maƙwabtansa sun ce an cigaba da dukkansa a ofishin rundunar ‘yan sanda wanda ya jawo mutuwarsa.

Sun ce, Usman da wasu mutane biyu da suka yi ƙoƙarin hana a kama shi duk suna tsare a ofishin ‘yan sandan. Sun ce su ma ‘yan sanda sun dake su tare da azabtar da su.

Advertisement

A cewar ɗaya daga cikin iyalan wanda ya rasu, Jamilu Haruna, Usman ya mutu ne a ofishin ‘yan sanda a ranar da suka kama shi saboda tsananin azabtarwa.

Ya ce, wannan lamari ya sosa zukatan da yawan mazauna unguwarsu da masu bin sa sallah saboda kashe shi da aka yi ba da haƙƙinsa ba.

Advertisement

“’Yan sanda sun ɗauki gawarsa zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a matsayin wanda ba su san shi ba, amma asibitin sun ƙi karɓar gawarsa. Daga nan ne suka tafi da gawar asibitin Abdullahi Wase, inda aka ajiya ta a ɗakin ajiyar gawarwaki.”

“Mu iyalansa, muna shigar da ƙorafi ga mahukunta rundunar ‘yan sanda ta hannun lauyanmu Adamu Abubakar (SAN) a yayin da ‘yan sanda ke cewa sun kama wasu daga cikin jami’ansu saboda rashin nuna ƙwarewa wajen gudanar da aikinsu kuma har sun fara bincike kan lamarin.”

Advertisement

“An dai binne mamacina ranar Juma’a bayan an gudanar da binciken gawa a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan sun biya Naira 90,000. Ya dai rasu ne a ranar 22 ga watan Satumba kuma an binne shi a ranar 26 ga watan bayan kammala wancan bincike na gawa wanda kotu ta ba da umarni da kuma amincewar ‘yan sanda. Muna sa rana sakamakon binciken gawar zai fito cikin ‘yan makonni masu zuwa,” in ji Haruna kamar yadda ya shaida wa PREMIUM TIMES.

A lokacin da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Haruna Kiyawa, bai samu amsa wayarsa ba haka kuma bai ba da amsar saƙon kar-ta-kwana da aka aike masa ba kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending