News
Ƴan Sanda A Indiya Sun Cafke Ɗan Najeriya Da Ya Damfari Mata Sama Da 100
Rundunar ƴan sanda a birnin Delhi na ƙasar Indiya ta kama wani ɗan Najeriya mai shekaru 29 da ake zargi da damfara mata sama da 100 ta hanyar nuna kansa a matsayin ɗan kasuwa ɗan ƙasar Koriya da ke zaune a Birtaniya a cikin wata manhajar koyon harsuna.
Jaridar Hindustan Times ta ruwaito cewa wanda ake zargi mai suna Stephane, wanda kuma yake amfani da sunayen ƙarya “Dominic” da “Duck Young,” an cafke shi ne a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, A wani gida da yake haya a unguwar Tilak Nagar da ke yammacin Delhi.
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Ma’aikata 100 Domin Kare Gandun Daji A fadin jihar
Rahoton ya ce Stephane da abokan aikinsa sun yi amfani da dabarun soyayya ta yanar gizo wajen yaudarar waɗanda suka fada tarkonsu.
A mafi yawan lokuta, wasu daga cikin abokan hadin gwiwar sun rika kiran waɗanda suka kamu suna bayyana kansu a matsayin jami’an gwamnati, suna kuma neman kuɗi domin a saki Stephane da ake cewa an tsare shi.
Wani lamari da ya bayyana damfarar shi ne na wata mata mai suna Anjali, wadda ta ce ta tura kuɗi har Rs 48,500 bayan wanda ake zargin ya faɗa mata cewa an tsare shi a filin jirgin saman Mumbai. Bayan haka ta fara samun kira daga wasu da suka ce jami’an shige da fice ne, suna neman ƙarin Rs 2 lakh, amma da ta ƙi, sai wanda ake zargin ya ɓace.
Ƴan sanda sun gano inda Stephane yake ta hanyar lambar waya, asusun banki, da bayanan shafukan sada zumunta. Lokacin da aka cafke shi, an gano waya ɗaya cike da ƙirarrun bayanai da hirarraki da mata fiye da 100.
A yayin tambayarsa, Stephane ya amsa cewa ya shiga Indiya tun 2019 da bizar yawon shakatawa na watanni shida, amma ya yi amfani da fasfo na Ivory Coast domin kauce wa takunkumin da ke kan ‘yan Najeriya a lokacin. Bayan ƙarewar bizar sa da rashin kuɗi, sai ya fara damfarar mutane ta yanar gizo
