Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi A jihar 

Published

on

Triumph

Majalisar Shura ta jihar Kano, wacce gwamnatin jihar ta kafa domin kula da harkokin wa’azi, ta sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu, wanda aka fi sani da Lawan Triumph, daga gudanar da wa’azi a jihar.

Sakataren Majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan a yau Laraba yayin wani taron manema labarai a Kano.

Advertisement

Gwamna Abba Ya Bukaci Shugaban Kasa Ya Sauya Kwamishinan Yansandan Kano 

Sagagi ya ce dakatarwar na da nufin bai wa Malam Lawan damar bayyana a gaban majalisar domin kare kansa kan zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman da ake ganin sun ƙunshi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

“An dakatar da Malam Lawan ne har zuwa lokacin da za mu kammala bincike da kuma sauraron bayanin sa a gaban majalisar. Wannan mataki shi ne mafi dacewa don tabbatar da adalci,” in ji shi.

Advertisement

Ya kuma yi gargadi ga ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji tsoma baki cikin batun, yana mai cewa dole ne a bar kwamitin ya kammala aikinsa cikin gaskiya da tsoron Allah.

Sakataren ya tabbatar da cewa Majalisar Shura za ta gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci, ba tare da nuna son rai ko wariya ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending