News
Wata Mata Ta Haifi Jariri Mai Fuska Biyu, Ido Hudu A Bauchi
Wani lamari mai ban mamaki da ya ɗauki hankalin al’umma ya faru a ƙauyen Magonshi da ke ƙaramar hukumar Katagum ta jihar Bauchi, inda wata mata mai suna Hannatu ta haifi jariri mai fuska biyu da kai guda, abin da likitoci suka bayyana a matsayin abu da ba kasafai ake gani ba.
An haifi jaririn ne a Babban Asibitin Gwamnati na Azare, inda aka gudanar da tiyata kyauta domin fitar da shi cikin koshin lafiya. Likitoci sun bayyana cewa irin wannan yanayi yana faruwa ne sau ɗaya kacal cikin mutum miliyan 10.
Dakarun Soji Sun Kama ’Yan Sandan Bogi Da Motoci 2 Makare Da Tabar Wiwi
“Mun karɓi lamarin da yardar Allah” — Mijin mahaifiyar jaririn
A tattaunawa da jaridar Aminiya, mijin Hannatu, Malam Bala Sa’idu, ya ce duk da jaririn bai zo da siffar da aka saba gani ba, sun rungumi lamarin da yardar Allah.
“Matata ta ɗauki cikin tsawon makonni 42 kafin haihuwa. Mun gode wa Allah da ya sauke ta lafiya, sannan muna godiya ga likitocin da suka taimaka ba tare da karɓar kuɗi ba,” in ji Bala.
Ya kuma bayyana cewa jaririn yana bukatar kulawa ta musamman saboda yanayin jikinsa, don haka suke roƙon gwamnatin jihar Bauchi da kungiyoyin agaji su taimaka musu wajen kula da lafiyar jaririn.
Likitoci sun bayyana mamaki
Dr. Bello Idris, babban likitan da ya jagoranci tiyatar, ya ce a tsawon shekaru da yake aikin likitanci bai taɓa ganin irin wannan haihuwa ba.
“Jaririn yana da kai guda, fuska biyu, idanu hudu, hanci biyu, baki biyu, kunne biyu, hannaye biyu da ƙafafu biyu. Amma bakin biyu sun zo a tsage, wanda hakan ke kawo ƙalubale wajen shayar da shi,” in ji shi.
Ya ce bayan mahaifiyar ta samu sauƙi, za a tura su zuwa Babban Asibitin Koyarwa na Tarayya (FUHSTA) da ke Azare domin ci gaba da duba lafiyar jaririn tare da gudanar da ƙarin bincike kan yanayinsa.
Kira ga gwamnati da masu hannu da shuni
Iyayen jaririn sun sake kira ga gwamnati, kungiyoyi da masu hannu da shuni da su taimaka wajen ganin jaririn ya samu kulawa ta musamman da zai taimaka masa wajen rayuwa cikin koshin lafiya.
Wannan lamari ya sake jaddada cewa ikon Allah ba ya da iyaka, kuma ya nuna cewa halittar Allah tana bayyana ta hanyoyi masu ban mamaki da suke burgewa dakuma koya darasi ga al’umma.
