News
Likitoci Sun Ciro Cokulan Ƙarfe 29, Burushi 19 Da Biro 2 Daga Cikin Wani Mutum
Likitocin tiyata a kasar Indiya sun gudanar da wani aiki da ya jawo hankalin duniya, bayan da suka ciro cokula 29 na ƙarfe, burushi 19 na wanke baki , da biro biyu daga cikin wani mutum.
Rahoton da jaridar Times Of India ta fitar ya ce mutumin, wanda asalin sa daga garin Bulandshahr, an kwantar da shi a wata cibiyar warkar da masu shaye-shaye a Ghaziabad kusan wata guda da ya gabata.
Amma daga bisani aka garzaya da shi asibiti bayan da ya fara korafin ciwon ciki mai tsanani.
Duban dan tayi da aka yi masa ya gano karafa da abubuwa masu kaifi da yawa a cikin cikinsa. Wannan ne ya sa likitoci, karkashin jagorancin Dr. Shyam Kumar, suka gudanar da aikin gaggawa a asibitin Hapur don ceto rayuwarsa.
Dr. Kumar ya bayyana cewa aikin tiyatar ya kasance “mai matuƙar rikitarwa da hatsari”, domin sun cire kowanne abu daya bayan daya cikin kulawa domin guje wa lalata wasu sassan jikinsa. Duk da hadarin da ke tattare da aikin, an kammala shi cikin nasara.
A cewar jaridar Hindustan Times, makamancin wannan lamari ya faru a shekarar 2022 a birnin Muzaffarnagar, inda aka ciro cokula 63 daga cikin wani mutum da ke fama da shaye-shaye. Haka kuma a 2019, wasu likitoci a Himachal Pradesh sun gano cokula, burushi, wuka da makulli a cikin wani marar lafiya da ke fama da tabin hankali.
