News
Wani Yaro Mai Shekara 15 Ya Nutse A Wani Kogi A Jigawa
Jami’an Hukumar kare kadarorin gwamnati da al’umma (NSCDC) reshen jihar Jigawa sun tabbatar da cewa wani yaro, Sunusi Abubakar, mai shekara 15 ya nutse a ruwa.
Mai magana da yawun hukumar, Badaruddeen Tijjani, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin jawabin da ya fitar a a garin Dutse a ranar Laraba.
Wata Mata Ta Banka Wa Kanta Wuta Har Lahira A Gidan Tafawa Balewa
Mista Tijjani ya ce, Abubakar, wanda mazaunin ƙauyen Gabari ne da ke masarautar Chamo, kuma ya nutse ne a ranar Talata a yayin da yake wanka a kogin.
Ya ce, sun samu yaron ne a mace a cikin kogin da ake kira “Mahayin gidan Toro” da ke kilomita 1.5 a kudancin ƙauyen Gabari.
Kafin kai wa ga gano yaron, sun samu wandonsa da takalmansa ne a yashe a bakin kogin.
“Kuma a cewar mahaifin yaron da ya rasu, ya je yin wanka ne a kogin da misalin ƙarfe 5 na yamma, sai dai daga baya an ji shiru bai dawo gida ba.”
”Nan take akaa shiga nemansa kafin daga baya da safe a kai ga gano inda yake,” ya faɗa.
A cewar kakakin NSCDC bayan gano gawar yaron wacce ba alamun wani rauni a cikinta, sai suka miƙa wa iyayensa domin a yi masa sutura.
Ya kuma buƙaci iyaye da masu kula da yara da shugabannin wannan al’umma da su gargaɗi yara da matasa da su ƙauracewa ɗabi’ar zuwa yin wanka a koguna masu haɗari domin kiyaye faruwar hakan a nan gaba.
Ya ba da tabbacin cewa rundunar a shirye take wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
