Connect with us

News

Dabarun Soji Sun Halaka Gwamman ‘Yanta’adda Tare Da Kame Ɓatagari 450

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rundunar tsaron Najeriya a yau Asabar, ta sanar da samun nasarar halaka gwamman ‘yanta’adda, tare da ceto fararen hula 180 da aka yi garkuwa dasu, baya ga kame ‘yanbindiga da sauran ɓata gari aƙalla 450 a watan Satumba kaɗai.

Haka zalika, rundunar ta ce ‘yanta’adda aƙalla 39 ne suka miƙa wuya tare da ajjiye makamansu, kana sun ƙwace bindigu, da harsasai da sauran ababen fashewa da dama.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Magance Ciwon Hawan Jini a Cibiyoyin Lafiya 208

Manjo Janar Markus Kangye, daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaron Najeriya ne ya sanar da nasarar da dakarunsu suka samu.

Markus ya ce dakarun tsaron sun kuma samu nasarar ƙwace akwatinan rediyo, da babura, da sauran ababen hawan dake taimakawa ‘yanbindigar wajen aikata ɓarna tare da jefa tsaron ƙasar cikin mummunan yanayi.

Advertisement

Ko a ƙarshen watan da ya gabata sai da shalwaktar tsaron Najeriya ta ce ta kama ƴanta’adda sama da 147 tare da kwato mutanen da aka yi garkuwa da su guda 39 cikin mako guda kawai a sassan ƙasar.

 

Advertisement

FRI HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending