News
Wasu Fusatattun Matasa Sun Kone Mutum 3 Kurmus Bisa Zargin Garkuwa
Wasu fusatattun matasa a garin Emu Orakwan da ke karamar hukumar Esan South-East a jihar Edo, sun kone wasu mutum uku kurmus bisa zargin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, bayan da wasu makiyaya da manoma suka hango mutanen da ake zargi a sansanin da ake kira Akabueze Camp.
Wani masanin tsaro mai suna Zagazola Makama ya bayyana cewa, waɗanda aka kashe ana zargin suna da hannu wajen kisan wata mata mai suna Hajiya Ogbonna, wadda aka kashe a ranar 1 ga Oktoba, inda aka tsinci gawarta a gona kusa da unguwa cike da raunin wuka da dama.
Bayan samun labarin mutuwar matar, mazauna yankin suka taru suka kai farmaki kan mutanen da ake zargi da laifin, kafin jami’an tsaro su isa wurin.
“Waɗannan mutane sun addabi yankinmu tsawon watanni. Suna yin garkuwa da mata, suna neman kudin fansa da ba za mu iya biya ba. Mun sha kai ƙara, amma babu sauyi — shi ya sa jama’a suka ɗauki doka a hannunsu,” in ji wani manomi daga garin Emu Orakwan.
Rahotanni sun ƙara tabbatar da cewa sojoji da ‘yan sanda sun isa wurin bayan an cinna wa mutanen wuta, inda suka tarar da su cikin mummunan hali. An garzaya da su asibitin gwamnati, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu gaba ɗaya.
Hukumomin tsaro na jihar Edo sun ce an fara bincike domin gano musabbabin lamarin, da kuma inda sauran ‘yan kungiyar garkuwar suke ɓoye.
