Connect with us

News

Yadda Jama’a Suka Daka Wawa Kan Kayan Tallafi A Nasarawa

Published

on

11868a66e00daf32

DAGA ZUBAIRU LAWAL, KEFFI

Taron rabon tallafi da Ministar Harkokin Mata ta Tarayyar Najeriya, Hajiya Iman Suleiman Ibrahim, ta shirya a ranar Juma’a domin al’ummar shiyyar Keffi, ya rikide zuwa tashin hankali bayan jama’a sun daka wawa a wajen taron.

Advertisement

An shirya rabon tallafin ne domin taimaka wa mata, marayu da marasa galihu, a wani yunkuri na rage radadin tattalin arziki a tsakanin talakawa.

Mutum Ɗaya Daga Cikin Takwas Na Fama Da Matsalar Taɓin Hankali A Najeriya  —Likita

Wajen taron, wanda aka gudanar a Keffi Square, ya cika makil da jama’a tun kafin fara rabon kayan. Kayan tallafin sun haɗa da buhunan shinkafa, kekunan ɗinki, zannuwa, tukwanen gas, injunan markaɗe da wasu kayan amfanin gida.

Advertisement

Sai dai rahotanni sun nuna cewa rabon bai gudana cikin tsari ba, lamarin da ya janyo turmutsutsi da rikici a tsakanin masu son karɓar tallafin.

Wani shaida ya ce, “Kowa yana ta kokarin karɓar nasa. Ba a daidaita rabon ba, hakan yasa mutane suka daka wawa har aka lalata wasu kayayyaki.”

Advertisement

A cewar wasu daga cikin mahalarta, da dama daga cikinsu sun tafi gida ba tare da sun samu komai ba, wasu kuma sun samu raunuka sakamakon cunkoso da tazgaro.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ta shiga tsakani domin kwantar da tarzomar, yayin da ba a samu rahoton rasa rai ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending