News
Mutum 10 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata a Mummunan Hadarin Mota A Titin Obajana
Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da cewa mutum 10 sun mutu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a daren Juma’a a hanyar Obajana zuwa Lokoja, jihar Kogi.
Kakakin hulɗa da jama’a na hukumar, Mista Olusegun Ogungbemide, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar .
Ya ce Babban Kwamandan FRSC, Malam Shehu Mohammed, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a yankin Apamaru.
A cewarsa, haɗarin ya haɗa da wata mota kirar Toyota Hiace mai lamba KTG 100YL, wadda ke ɗauke da fasinjoji maza 21.
Binciken farko na FRSC ya gano cewa gudu fiye da ƙa’ida da kuma yin ƙetare hanya ba bisa ƙa’ida ba daga direban motar ne ya jawo haɗarin.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Fisayo da ke Obajana, yayin da aka mika gawarwakin waɗanda suka mutu ga iyalansu domin gudanar da jana’iza.
-
News7 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
