Connect with us

News

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Hukuncin Daurin Rai-da-Rai Ga Duk Wanda Aka Kama Da Lalata Yara Ƙanana

Published

on

FB IMG 1753200680601

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin doka da ke tanadar da hukuncin daurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yara ƙanana — matakin da ke nufin tsaurara hukunci ga masu aikata wannan mummunan laifi a faɗin ƙasar.

A zaman majalisar da aka gudanar a ranar Talata, ‘yan majalisar sun bayyana cewa lalata da yara ƙanana babbar barna ce “mai iya lalata rayuwar yaro ko yarinya har abada,” don haka ya zama wajibi hukuncin ya kasance mai tsauri domin ya zama izina ga wasu.

Advertisement

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargaɗi

Da farko, Sanata Adams Oshiomhole ya gabatar da shawarar a sanya hukuncin daurin shekaru 20 ga masu aikata irin wannan laifi. Sai dai majalisar ta yi adawa da hakan, tana ganin hukuncin bai da nauyin da ya dace da girman laifin ba.

Daga nan sai Sanata Adamu Aliero ya gabatar da sabuwar shawara, inda ya nemi a hukunta duk wanda aka same shi da laifin lalata da yara da daurin rai-da-rai, wadda Sanata Olamilekan Yayi ya mara wa baya.

Advertisement

Bayan tattaunawa da amincewar baki ɗaya daga cikin sanatocin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa:

“Majalisar Dattawa ta yanke shawarar cewa daga yau duk wanda ya aikata laifin lalata da yara a Najeriya, za a yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da wani zaɓin biyan tara ba. Kowa ya sani.”

Advertisement

Majalisar ta ce wannan mataki zai taimaka wajen kare rayuwar yara da rage yawaitar fyade da cin zarafin yara da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending