News
Kwamishinan Tsaro Na Gombe Kanal Abdullahi Bello Ya Rasu A Hatsarin Mota
Gwamnatin Jihar Gombe ta shiga jimami bayan rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello mai ritaya, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe a ranar Juma’a.
A cewar wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, marigayi Kwamishinan ya rasu tare da mai tsaronsa, Sajan Adamu Husaini, yayin da suke dawowa daga Maiduguri, Jihar Borno, bayan halartar taron shiyyar Arewa maso Gabas kan shirin “National Disarmament, Demobilization and Reintegration (DDR).”
Misilli ya ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana marigayi Kanal Bello a matsayin jarumi mai cikakken kishin ƙasa, wanda ya yi aiki da sadaukarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron cikin gida a Gombe.
A halin yanzu, direban Kwamishinan na karɓar jinya bayan raunukan da ya samu a hatsarin.
Gwamnatin ta ce za a sanar da lokacin jana’izar marigayin da mai tsaronsa nan gaba kaɗan.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News18 hours ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
