News
Gwamna Radda Ya Yi Sauye-sauye A Majalisar Zartarwarsa
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya amince da sauye-sauyen manyan jami’an gwamnati da kuma naɗin sabbin masu ba da shawara biyu, domin ƙara inganta gudanar da ayyukan gwamnati a fannonin daban-daban na jihar.
A cewar sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammad, ya fitar a ranar Juma’a, sauye-sauyen sun fara aiki nan take, tare da nufin ƙarfafa inganci da daidaita tsarin aiki a cikin gwamnati.
Kwamishinan Tsaro Na Gombe Kanal Abdullahi Bello Ya Rasu A Hatsarin Mota
Daga cikin waɗanda sauye-sauyen suka shafa akwai Adnan Nahabu, wanda aka naɗa a matsayin kwamishinan ilimi na manyan makarantu, sana’o’i da fasaha, yayin da Farfesa Ahmad Muhammad Bakori ya koma shugabantar sabuwar ma’aikatar kiwon dabbobi.
Haka kuma, Aliyu Lawal Zakari daga Ma’aikatar Matasa da Wasanni ya koma Ma’aikatar Noma, sai Zainab Musa Musawa wacce aka ɗauke ta daga Ma’aikatar Ilimi zuwa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
Yusuf Suleiman Jibia ya karɓi ragamar Ma’aikatar Ilimi daga Tushe da Sakandare, yayin da Injiniya Surajo Yazid Abukur ya zama Kwamishinan Matasa da Wasanni.
Sannan tsohuwar Darakta a Hukumar Bunƙasa Kasuwanci ta Jihar Katsina, Aisha Aminu, ita ce sabuwar Kwamishinar Harkokin Mata.
Bugu da ƙari, Gwamna Radda ya naɗa Hadiza Abubakar Yar’adua a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan abinci mai gina jiki da walwalar jama’a, da kuma Isa Muhammad Musa a matsayin mai ba da shawara kan al’adu da ɗabi’u.
Gwamnan ya bukaci sabbin jami’an da su kasance masu kishin aiki, tare da bin manufofin gwamnatinsa ta “Building Your Future”, wacce ta mayar da hankali kan inganta ilimi, noma, lafiya, matasa, mata da walwalar jama’a a jihar.
