News
Fashewar Tukunyar Gas Ya Lalata Shaguna da Dama a Kasuwar Orisunmibare
Wata fashewar tukunyar gas da ta auku ranar Lahadi ta kone shaguna da dama a Kasuwar Orisunmibare, kusa da Baale Street, a unguwar Orile-Iganmu, jihar Lagos.
Rahotanni sun nuna cewa fashewar ta faru da misalin ƙarfe 2:13 na rana, inda ta janyo asarar kaya masu daraja da kimanin miliyoyin naira.
Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba
An bayyana cewa fashewar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da gas, inda ake zargin ana ajiye bututun gas iri-iri ba bisa ka’ida ba.
Mrs. Margaret Adeseye, Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Lagos, ta ce jami’an su sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka samu nasarar shawo kan wutar kafin ta ƙara yaduwa.
Ta kara da cewa: “Ba a rasa rayuka ba, sai mutum guda kawai da ya ji rauni kadan a hannunsa.”
Hukumomi sun yi kira ga ‘yan kasuwa da su bi ka’idojin ajiye kayan gas don kauce wa irin wannan hatsari nan gaba.
