Connect with us

News

K-MAN Ta Nuna Jimami Bisa Hatsarin Mota Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12 A Kano 

Published

on

1761592684022750 0

Kungiyar Kano Media Advocacy Network (K-MAN) ta bayyana alhini da tausayinta ga iyalan waɗanda suka rasu a hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Wudil, jihar Kano, ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa motar Kano Line ce ta yi hatsarin, inda abin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, lamarin da ya girgiza al’umma a yankin.

Advertisement

Kotu Ta Wanke Ango Da Ƴanuwansa 11 Daga Zargin Kashe Jami’ar Ƴan Sanda

A cikin sanarwa, K-MAN ta ce wannan lamari abin bakin ciki ne, kuma ya tunatar da jama’a muhimmancin bi dokokin hanya domin kiyaye rayuwar ɗan adam.

Kungiyar ta mika ta’aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, iyalan waɗanda suka rasu, da kuma al’ummar Kano baki ɗaya.

Advertisement

A lokaci guda, K-MAN ta yaba wa Gwamnan kan yadda yake gudanar da manyan ayyukan gyaran hanyoyi da inganta rayuwar al’umma, wanda ya sa Kano ta zama cibiyar ayyukan raya kasa.

Kungiyar ta ce irin wannan jajircewar gwamnati zai taimaka wajen rage hatsarori a hanyoyi da tabbatar da aminci a zirga-zirgar ababen hawa.

Advertisement

A ƙarshe, K-MAN ta roƙi direbobi da sauran masu amfani da hanyoyi da su kasance masu bin dokokin hanya da ka’idojin tsaro, tare da addu’ar Allah Ya jikan waɗanda suka rasu, Ya ba iyalansu haƙuri.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending