News
Kotu Ta Yanke Wa Barayin Kebil Hukuncin Shekara 2 Da Wata 10 A Gidan Yari A Kano
Kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare a birnin Kano ta yanke hukuncin daurin shekara biyu da wata goma ga wasu matasa biyu da aka kama da laifin satar kebil na wutar lantarki daga taransfoma, ba tare da zaɓin tara ba.
Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne Muhammad Ibrahim da Ahmed Sulaiman, inda kotu ta kuma umarce su da su biya rankon kebil ɗin da suka sata.
Ibrahim Little: Ɗan Siyasa Mai Gaskiya Da Kwarewa, Jagora Mafi Cancanta Da Zai Inganta Kano A 2027
Rahotanni sun ce asirin barayin ya tonu ne lokacin da suke raba kudin abin da suka sata a unguwar Na’ibawa Yamma, inda jama’a suka gano su, suka sanar da hukumomi.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Abba Malam, tare da wasu mazauna, ne suka shigar da korafi a ranar 20 ga watan Oktoba, 2025, inda suka zargi barayin da satar kebil daga taransfoma na yankin.
An gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhuma uku: haɗa kai wajen aikata laifi, sata, da kuma samun makami mara kyau.
Bayan an karanta musu kunshin tuhuma, mutanen biyu sun amsa laifinsu, lamarin da ya sa kotu ta yanke musu hukunci kamar haka:
Laifin haɗa kai: daurin wata biyar, tare da zaɓin tara na ₦5,000.
Laifin mallakar makami: shekara biyu a gidan yari, babu zaɓin tara.
Laifin sata: wata goma a gidan yari, babu zaɓin tara.
Mai shari’a Munzali Idris Gwadabe ne ya yanke hukuncin, inda ya ce hukuncin zai fara aiki daga ranar da aka kama su.
