News
Yan ta’adda na barazanar kawo mana harin bama-bamai a majalisar Wakilai Garba Diso
Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na majalisar wakilai, Garba Muhammad Ɗiso, ya ce sun samu barazana daga yan ta’adda cewa za su kai hari da bama-bamai a ginin majalisar.
Ya bayyana hakan ne a yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin dokar kafa hukumar tsaron majalisar dokoki wadda ke da nufin inganta tsarin tsaro da kare yan majalisa, ma’aikata da baki da ke zuwa majalisar.
A cewarsa, majalisar ta dade tana fama da matsalolin tsaro da suka hada da satar motoci da babura, lalata kayan gwamnati, yin amfani da katin karya da kuma shigowar baki marasa rajista cikin harabar majalisar.
Dan majalisar ya ce akwai gaggawar bukatar karfafa tsaron majalisar don hana faruwar abin da ka iya haifar da matsala ga tsarin dimokuradiyya.
PREMIER RADIO
