Connect with us

News

Hadarin Jirgin Sama Yayi Ajalin Dukkan Fasinjojin Cikinsa

Published

on

74523881 803
Fasinjoji 10 da ke cikinsa 'yan kasar Hungary ne, sai Jamusawa 2 da kuma direban jirgin 'dan kasar Kenya

Hadarin jirgin saman kasar Kenya mai suna Mombasa Air Safari, ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan fasinjoji 11 da ke cikinsa, wadanda Jamusawa ne da ‘yan kasar Hungary, kamar yadda kamfanin jirgin ya sanar a wannan Talata.

Shugaban kamfanin John Cleave, ya ce fasinjoji 8 ne ‘yan kasar Hungary sai Jamusawa 2, da kuma direban jirgin ‘dan kasar Kenya.

Advertisement

’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata Tambuwal

Jirgin ya taso ne da asubahin wannan rana ta Talata daga yankin Diani na kasar da ke zama matattarar shakatawar ‘yan yawon bude ido, a kan hanyarsa ta zuwa wurin shakatawa na Maasai Mara National Park da ke yankin Kichwa Tembo.

Tuni hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Kenya ta kaddamar da binciken musabbabin faruwar hadarin.

Advertisement

Ko a cikin watan Agustan 2025 makamancin hadarin ya halaka mutane 6, tare da jikkata wasu 2 a Nairobi babban birnin kasar.

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending