Connect with us

Uncategorized

‎Kano: ’Yan Yi wa Ƙasa Hidima Sun Yi Gangamin Tsabtace Muhalli A Sakatariyar Audu Bako ‎

Published

on

IMG 20251101 WA0005

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

‎’Yan yi wa ƙasa hidima NYSC da ke gudanar da aikinsu a Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano sun gudanar da gangamin tsabtace muhalli a harabar Sakatariyar Audu Bako, da nufin ƙarfafa tsafta da inganta yanayin aiki a ma’aikatar.

‎Da take jawabi yayin aikin tsaftar, Daraktar Wayar da Kai ta Ma’aikatar Muhalli, wacce ta wakilci Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Hashim Muhammad, ta ce wannan aikin na nuna yadda matasa ke ba da gudunmawa wajen samar da muhalli mai tsafta.

‎‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kasashen Waje 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

‎“’Yan yi wa ƙasa hidima sun nuna kishin ƙasa da himma wajen kare muhalli. Wannan aiki yana cikin manufofin gwamnati na tabbatar da tsafta da kare lafiyar jama’a,” in ji ta.

‎Ta ƙara da cewa Kwamishinan Ma’aikatar yana da shirin tabbatar da tsafta a dukkan sassan jihar Kano, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftace muhalli.

‎A nasa bangaren, jagoran ’yan yi wa ƙasa hidiman ya bayyana cewa sun gudanar da aikin ne domin nuna irin abin da suka koya a lokacin aikinsu na shekara ɗaya a ma’aikatar.

Advertisement

‎‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kasashen Waje 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

‎ “Mun shirya wannan aiki ne a matsayin bankwana, da kuma damar nuna gudunmawar da muka bayar wajen inganta tsaftar muhalli a wurin aiki,” in ji shi.

‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kasashen Waje 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

‎Wakiliyar mu Safiya Muhammad Usman ta ruwaito cewa ’yan yi wa ƙasa hidiman sun yi kira ga jama’ar Kano da su ƙara mayar da hankali wajen kula da tsaftar muhallinsu da samar da magudanar ruwa, domin kare lafiyar al’umma da hana yaduwar cututtuka.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending